Wasu Tagwayen Bama-Bamai Sun Tashe Jihar Zamfara Kwanaki Bayan Irin Wannan Lamarin
Bama-baman sun tashi ne a kan titin Dansadau da Malamawa da kuma wani kan titin Malele, duk a gundumar Dansadau.
Kwanaki kadan bayan tashin bama-bamai a jihar Zamfara, lamarin da ya yi sanadin mutuwar matafiya tare da jikkata wasu da dama, wasu bama-baman da ba su gaza biyu ba sun tashi a wurare daban-daban a gundumar Dansadau da ke karamar hukumar Maru ta jihar.
Bama-baman sun tashi ne a kan titin Dansadau da Malamawa da kuma wani kan titin Malele, duk a gundumar Dansadau
An kuma bayyana cewa bama-baman da suka tashi a kan titin Malamawa da Malele sun tashi ne a lokaci guda amma ba a samu asarar rai ba.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, wani mazaunin garin mai suna Nuhu Babangida ya ce fasinjojin da ke cikin wata babbar mota kirar Canter da za ta je kasuwar mako-mako ta Dansadau a ranar Juma’a sun tsallake rijiya da baya bayan da motar da ke dauke da hatsi ta tayar da bam din.
Sa bam din shine karo na uku da za aka dasa bam a hanyar Dansadau cikin mako guda.
A ranar Larabar da ta gabata ne aka yi fargabar mutuwar mutane 12 bayan da wata bam ya tashi a wata gada a kauyen Yar Tasha.
A ranar Lahadin da ta gabata kuma, wata na’urar da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ce ta dasa ta tarwatse da wata motar bas mai dauke da kujeru 18, inda ta kashe direban, wanda shi kadai ne ke cikin motar.
A baya ClockwiseReports ta rahoto cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da cewa sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda, Lakurawa ce ke da hannu wajen tayar da bama-bamai da aka yi a wasu kauyuka biyu a gundumar Dansadau, karamar hukumar Maru (LGA) ta jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Shehu Dalijan ya tabbatar da hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai.