Jam’iyyar NNPP ta garzaya kotun koli domin kalubalaantar hukuncin kotun daukaka kara na zaben gwamnan Kano

IMG 20230618 WA0183
IMG 20230618 WA0183

Jam’iyyar NNPP ta garzaya kotun koli domin daukaka kara kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan zaben gwamnan Kano, wadda ta zartar da hukuncin cewa Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC ne ya ci zabe.

A cikin sanarwar daukaka karar da Jaridar Solacebase ta gani, jam’iyyar NNPP ita ce mai shigar da kara sai Abba Kabir Yusuf da jam’iyyar APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta wadanda ke kunshe cikin kunshin shari’ar.

Jaridar SOLACEBASE ta kuma rawaito cewa kotun daukaka kara a ranar Juma’ar da ta gabata ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke na tsige Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano tare da bayyana Nasiru Yusuf Gawuna na APC a matsayin wanda ya yi nasara.

Jam’iyyar NNPP ta daukaka kara kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan wasu dalilai guda goma da bayyana da rashin adalci.

Jam’iyyar ta ce alkalan kotun daukaka kara sun yi kuskure a shari’a tare da nuna rashin adalci ga wadanda suka shigar da kara.

Muna tafe da Karin bayani…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here