Kwararren dan jarida Dakta Sule Ya’u Sule zai kaddamar da Littafi

Book on Strategic Communication 750x430
Book on Strategic Communication 750x430

Kwarraren dan jarida kuma shehin Malami a fannin Jarida Dakta Sule Ya’u Sule, zai kaddamar da sabon littafinsa da ya rubuta akan hanyoyi da dabarun sadarwa a ranar Asabar, 7 ga watan Disamba mai zuwa.

Littafin mai suna: “An Introduction to Strategic Communication”, za a gabatar da shi ga jama’a a Otal din NICON Luxury, da ke area 11, a babban birnin tarayya Abuja.

Da yake bayyana wa Jaridar PRNigeria abin da sabon littafinsa ya kunsa Dakta Sule Ya’u Sule, wanda kuma babban malami ne a tsangayar Sadarwa ta Jami’ar Bayero dake Kano, yace sabon littafin nasa zai baiwa kwararrun marubuta labarai da masu bincike da dalibai cikakkiyar damar fahimta da hangen nesa kan abin da dabarun sadarwa ke tattare da su.

Dakta Sule Ya’u, ya kuma bukaci masu sana’ar wallafa bayanai da su fito da wani abu wanda zai taimakawa marubuta masu tasowa, a ayyukan sun a wallafa.

Za a kaddamar da littafin ne da safiyar ranar, yayin da ake sa ran bayar da lambar yabo gwarzon masu Magana da yawun shugabanni wato Spokespersons Communications Awards da kuma bayar da lambar yabo ta Security and Emergency Management Awards, su kuma da rana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here