Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja, ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar Nassarawa Abdullahi Sule.
Hukuncin na baya baya nan , ya soke hukuncin da Kotun sauraren kararrakin zabe tayi na soke zaben Gwamnan a baya data yi a Ranar 2 fa watan Oktobar da ya gabata , Inda ta ayyana David Ombugadu , na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.
Da suke bayyana hukuncin a yau Alkalan guda Uku , sun bayyana cewar Kotun ta baya tayi kuskuren sauke zaben gwamnan na jihar ta Nassarawa.












































