Kano ta zama abin koyi wajen aiwatar da manufofin sauyin yanayi a taron nahiyar Afirka

WhatsApp Image 2025 10 09 at 19.25.27 750x430

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya tabbatar da kudirin gwamnatin jihar na ci gaba da kare muhalli da tabbatar da adalci a harkokin sauyin yanayi a fadin Afirka.

Dakta Hashim ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake gabatar da jawabi a babban taron nahiyar Afirka da aka shirya domin tattaunawa kan hanyoyin tabbatar da dorewar muhalli da adalcin sauyin yanayi na 2025 wanda aka gudanar a birnin Nairobi na ƙasar Kenya.

Taron wanda hukumar ALN Kenya tare da Cibiyar kula da Sauyin Yanayi ta Certa Foundation daga ƙasar Rwanda suka shirya, ya haɗa manyan jami’an gwamnati, masana, shugabannin ƙungiyoyin farar hula da abokan ci gaba daga kasashen Afirka da ma wajen nahiyar, karkashin taken “Ƙarfafa kula da sauyin yanayi don gina ƙauyuka da birane masu tasiri.”

Kwamishinan, wanda ya wakilci jihar Kano, ya tunatar da cewa jihar ta karɓi bakuncin taron Climate Justice Summit a watan Yulin 2025, wanda ya tabbatar da Kano a matsayin abin koyi na shugabanci mai adalci a matakin jiha a Najeriya da ma Afirka.

Ya ce wannan sabon taro yana ci gaba da jan hankalin ƙasashe kan muhimmancin haɗin kai domin magance matsalolin sauyin yanayi kamar dumamar yanayi, ambaliyar ruwa, fari, da lalacewar ƙasa waɗanda ke barazana ga rayuwar jama’a, abinci, kiwon lafiya da tattalin arziki.

Dakta Hashim ya jaddada cewa adalcin sauyin yanayi bai kamata ya tsaya ga ƙa’idoji kawai ba, sai dai ya zama mai maida hankali kan jama’a, musamman wajen haɗa mata, matasa, masu nakasa, manoma ƙanana, da ma’aikatan tsaftar gari cikin shirin yanke shawara.

Haka kuma, kwamishinan ya bayyana mahimman fannoni da taron ya mayar da hankali a kansu, kamar ƙarfafa tsarin doka da mulki, tallafawa sabbin fasahohin noma da kare muhalli, rage sharar yakin kamfanoni da kuma tabbatar da samun daidaito a amfani da makamashin zamani.

A ƙarshe, Dakta Hashim ya yi kira ga mahalarta taron da su tabbatar da cewa tattaunawar su ta kai ga sakamakon da zai amfanar da al’umma baki ɗaya, yana mai cewa, ya zama wajibi a gina Afirka mai adalci, mai mutunci, wadda za ta ba wa al’ummarta dama cikin kowane mataki nakare muhalli.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here