Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kawo ƙarshen tarin bashin ƙarin girma da aka samu a hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatarsa, tare da amincewa da biyan tsofaffin Kwanturola Janar da Mataimakan Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa albashi har tsawon rayuwarsu.
Tunji-Ojo ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin bikin rufe horo na musamman kan tsarin kula da iyakoki da gudanar da harkokin shige da fice (BCIMS), wanda aka gudanar a hedikwatar Hukumar Shige da Fice da ke Abuja.
Read also: Gwamna Makinde ya gabatar da shedar kama aiki ga sabon Alaafin na Oyo
Ya yaba wa Tinubu bisa magance matsalar jinkirin ƙarin girma, inda ya bayyana cewa aƙalla jami’ai 50,000 sun samu sabon matsayi da ƙarin girma cikin shekaru uku.
“Wannan abu bai taɓa faruwa ba a baya, amma Tinubu ya yi shi. Ya kuma ƙara yawan ɗaukar sabbin ma’aikata, inda yanzu ake ɗaukar aƙalla mutane 40,000 a lokaci guda.
“Idan aka zo batun ƙarin albashi, Shugaban Ƙasa ya yi hakan. Haka kuma, ya ƙara alawus ɗin haɗari da na musamman,” in ji shi.
Tunji-Ojo ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasar bisa jajircewarsa wajen inganta jin daɗin jami’an da ke aiki da waɗanda suka yi ritaya, musamman ta hanyar ƙara kuɗin fansho na tsofaffin Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice.
Read also: NiMET ta yi hasashen samun ruwan sama da gajimare na tsawon kwana uku a Najeriya
Ya ce a baya, tsofaffin shugabannin hukumar na karɓar fansho kusan naira 130,000, wanda bai wadatar ba.
Ya ƙara da cewa, “Amma me Shugaban Ƙasa ya yi? Ya sanya hannu tare da amincewa da biyan Kwanturola Janar da Mataimakan Kwanturola-Janar albashi har tsawon rayuwarsu.
“Wannan shugaban ƙasa ya kula da hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar fiye da kowane shugaban ƙasa a tarihin Najeriya. Ya ba ku duk abin da yake da shi.
Ministan ya ce Tinubu ya fahimci cewa ba zai ci gaba da zama a kan mulki har abada ba, amma cibiyoyin gwamnati za su ci gaba da wanzuwa, don haka abin da ya fi muhimmanci shi ne abin da za a gada kuma a miƙa wa al’ummomi masu zuwa.
Read also: NAPTIP ta tseratar da wasu mata 13 da za ayi safarar su zuwa Iraqi
NAN













































