An shiga fargaba a filin jirgin saman Abuja a ranar Alhamis bayan ƙofar wani jirgin sama ƙirar CL60 da kamfanin Triton Aviation ke sarrafawa ta fita a lokacin da yake shawagi a sararin samaniya, lamarin da ya tilasta wa matuƙan jirgin saukar gaggawa jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Bayanan da aka tattara sun nuna cewa jirgin mai lambar rajista T7-SEI da lambar tashi DWC052 yana kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas lokacin da lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:20 na yamma.
Read also: Gwamnatin tarayya za ta binciki yadda Fursunoni suka fasa gidan yari a Kogi
Wani rahoton aukuwar lamarin da jaridar The Punch ta rawaito ya nuna cewa matuƙan jirgin sun sanar da hasumiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama cewa wata ƙofa ta buɗe yayin da suke shawagi a sararin samaniya. Hakan ya sa jami’in kula da jiragen sama ya umurci jirgin da ya dawo Abuja domin yin saukar gaggawa.
Rahoton ya ƙara da cewa jirgin ya tashi daga layin sauka da tashin jiragen sama mai lamba 22 da ƙarfe 4:17 na yamma agogon UTC.
Rahoton ya ce jirgin yana da nisan mil uku daga filin jirgin, kuma yana tashi zuwa tsayin ƙafa 3,000 lokacin da matuƙan jirgin suka aika da saƙon neman agajin gaggawa, inda suka ce “Mayday, Mayday, Mayday.”
Bayan samun wannan saƙo, an gaggauta sanar da jami’an kashe gobara da masu aikin ceto na filin jirgin, da kuma jami’an lafiya, inda aka shirya su domin tunkarar duk wani yanayi na gaggawa.
Haka kuma, an umurci jami’an kashe gobara da masu aikin ceto da su tsaya a wuraren da aka ware domin jiran dawowar jirgin.
Read also: Gobara ta tashi a Fadar Sarkin Kano ta Kofar Kudu
Rahoton ya bayyana cewa da misalin ƙarfe 4:29 na yamma agogon UTC, yayin da suke tattaunawa da hasumiyar kula da jiragen sama ta Abuja, matuƙan jirgin sun tambayi jami’an ko za su iya tabbatar da cewa ƙofar ta buɗe.
Rahoton ya ce, “Jami’in kula da zirga-zirgar jiragen sama da ke bakin aiki ya yi ƙoƙarin duba jirgin da na’urar hangen nesa, amma bai iya tabbatar da halin da ƙofar take ciki ba saboda yadda jirgin yake a lokacin.
“Daga bisani, an sanar da matuƙan jirgin cewa jami’in bai iya tabbatar da lamarin ta hanyar gani ba.”
Daga ƙarshe, jirgin ya yi nasarar sauka lafiya a titin sauka da tashin jiragen sama mai lamba 22 da misalin ƙarfe 4:34 na yamma, kimanin mintuna 14 bayan matuƙan jirgin sun aika da saƙon neman agajin gaggawa.
Bayan saukar jirgin, jami’in kula da zirga-zirgar jiragen sama da ke bakin aiki ya bayyana cewa ƙofar ta fice daga jikin jirgin, abin da ya tabbatar da girman haɗarin da ya faru.
Daga nan ne aka ja jirgin zuwa wani ɓangare na filin ajiye jiragen sama na ƙasashen waje, inda aka ajiye shi tare da taimakon wani jami’in da ke jagorantar yadda jiragen ke motsawa a filin jirgin.
A wani ɓangare kuma, wani bidiyo da jaridar The Punch ta samu ya nuna ƙofar da ta ɓace, wadda rahotanni suka ce wasu manoma ne suka gano ta a wata gona da ke yankin Abuja.












































