Tinubu ya mayar da Babban Sakataren da aka dakatar

Bola Bola Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya mayar da Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗi (Ayyuka na Musamman), Mohammed Danjuma, kan muƙaminsa.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Olumuyiwa Abel, ne ya sanar da amincewar shugaban ƙasar cikin wata wasiƙa mai ɗauke da ranar 22 ga Oktoban 2026.

A cewar wasiƙar, mayar da Danjuma kan muƙaminsa ya fara aiki ne daga ranar 21 ga Oktoban 2026, bayan dakatar da shi sakamakon binciken ayyukan wata hukuma da ake zargin ta yi iƙirarin kasancewa ta gwamnati.

Wasiƙar ta bayyana cewa an dakatar da Danjuma ne a ranar 21 ga Agustan 2026, tare da wasu manyan sakatarori biyu, bayan wani rahoto da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffuka Masu Alaƙa (ICPC) ta fitar kan ayyukan wata hukuma mai suna National Brands Development and Made in Nigeria Special Project Office.

Ana zargin cewa George Buchi Nwabueze ne ya taimaka wa hukumar tare da zargin sa hannun wasu ma’aikatan gwamnati a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

“Bayan gudanar da binciken da ya dace, Shugaba Tinubu ya amince da ɗage dakatarwar da aka yi wa Danjuma, tare da umartar sa da ya koma bakin aikinsa bisa tanade-tanaden dokokin ma’aikatan gwamnati, ƙa’idojin da suka dace da kuma ƙa’idojin ɗabi’ar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.

“Mayar da shi kan muƙaminsa ya fara aiki ne daga ranar 21 ga Oktoban 2026.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here