SERAP ta maka NBC a Kotu kan dakatar da wakar Eedris ta ‘Tell Your Papa’

NBC 750x430

Kungiyar da ke rajin kare hakkin dan Adam da tattalin arziki da tabbatar da daidaito a ayyukan gwamnati (SERAP) ta maka hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC a gaban kotu kan dakatarwar da ta yiwa wakar Eedris Abdulkareem mai suna ‘Tell Your Papa’ ba bisa ka’ida ba.

Waƙar, wacce ake zargi da sukar manufofin tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu, an hana watsa ta a shirye-shiryen rediyo da TV saboda yanayin rashin amincewa, inda NBC ta ba da misali da cewa a cikin waƙar an yi cin zarafi da wuce ka’idodin da zai bada dama ya yaɗa a gidajen rediyo da TV.

A cikin karar mai lamba FHC/L/CS/797/2025 da ta shigar a ranar Alhamis din da ta gabata a babbar kotun tarayya da ke Legas, SERAP na neman kotun ta ba da umarnin soke dokar haramta wakar Eedris Abdulkareem mai suna ‘Tell Your Papa’, saboda rashin jituwa da kuma sabawa ‘yancin fadin albarkacin baki da samun bayanai, da ‘yancin yada labarai da kowanne dan kasa ke da shi.

SERAP na neman umarnin kotu kan ta bada dawwamammiyar doka da za ta hana hukumar NBC ta tarayya ko kuma wata hukumanko mutum ko gungun jama’a hana yada wakar Eedris Abdulkareem a dukkanin gidajen yada labarai da sauran kafafen yada labarai da makamantan haka a Najeriya.

Karin karatu: SERAP ta ba wa NBC wa’adin sa’o’i 48 ta janye dakatarwar da ta yiwa wakar Eedris Abdulkareem

SERAP tana kuma neman bayyana cewa umarnin NBC, wanda aka fitar ta wata wasika mai kwanan wata 9 ga Afrilu 2025 zuwa ga dukkan gidajen watsa labarai a Najeriya, na hana watsa wakar Eedris Abdulkareem haramun ne kuma bai dace da ‘yancin fadin albarkacin baki da samun bayanai, da ‘yancin yada labarai ba.

Matakin da hukumar ta NBC ta dauka ba bisa ka’ida ba ne, ba bisa ka’ida ba, kuma ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya, domin ya saba wa tanadin sashe na 39 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, da sashe na 9 na yarjejeniya ta ƴancin dan adam da Jama’a na Afrika, da kuma sashi na 19 na yarjejeniyar kasa da kasa kan ‘yancin jama’a da na siyasa.

Sai dai ba a sanar da ranar da za a saurari karar ba.

Kolawole Oluwadare

Mataimakin Darakta SERAP

20/04/2025

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here