SERAP ta ba wa NBC wa’adin sa’o’i 48 ta janye dakatarwar da ta yiwa wakar Eedris Abdulkareem

Eedris Abdulkareem

Kungiyar kare hakkokin dan adam da kuma rajin yattalin arziki (SERAP) ta bada wa’adin sa’o’i 48 ga gwamnatin tarayya da hukumar kula da kafafen yada labarai ta Kasa (NBC), inda ta bukaci a gaggauta janye dakatarwar da aka yiwa sabuwar wakar nan da ta kira haramtacciyar wakar zanga-zanga ta Eedris Abdulkareem mai suna “Ka Fada wa Baba.”

A cikin wata sanarwa da ta fitar a dandalinta na X a ranar Alhamis, SERAP ta bayyana haramcin a matsayin cin zarafin ‘yancin fadin albarkacin baki tare da gargadin daukar matakin shari’a idan ba a soke umarnin a cikin wa’adin da ta kayyade ba.

SERAP ta ce “Dole ne gwamnatin Tinubu ta yi gaggawar janye haramcin da hukumar NBC ta yi na hana gidajen rediyo da Talabijin na Najeriya watsa sabuwar waka ta Eedris Abdulkareem.”

A cewar SERAP “Za mu gamu a kotu idan ba a sauya dokar ba a cikin awanni 48.”

Labari mai alaƙa: NBC ta dakatar da Eedris Abdulkareem daga yaɗa wakarsa ta “Tell Your Papa” a gidajen rediyo da Talabijin

SolaceBase ta ruwaito cewa NBC, a cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan Afrilu 9, 2025, kuma mai dauke da sa hannun Susan Obi, Daraktar kula da watsa Labarai, ta ayyana wakar a matsayin wadda ta haramta a yada, har ma hukumar ta buga misali da sashe na 3.1.8 na kundin tsarin yada labarai na Najeriya, wanda ya haramta yada abinda ake ganin ya saba wa mutuncin jama’a.

Eedris Abdulkareem, wanda ya shahara da wakokinsa na zamantakewa da siyasa, ya dade yana amfani da dandalinsa wajen yin tsokaci kan harkokin mulki, cin hanci da rashawa, da adalci a zamantakewa. Sabuwar waƙarsa mai suna “Ka Faɗa wa Babanka,” rahotanni sun ce yana sukar gwamnati mai ci kan matsalar tattalin arziki da gazawar gwamnati.

Masu suka dai sun bayyana matakin na NBC a matsayin wani yunƙuri na murkushe ƴancin fasaha, lamarin da SERAP ta sanar a cikin sanarwar ta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here