Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Kaduna.
Daga cikin waɗanda suka raka Atiku akwai tsofaffin gwamnonin jihohin Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da na Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu jiga-jigan ƴansiyasa.
Atiku ya wallafa bidiyon ziyarar a shafinsa na Facebook, sannan ya rubuta cewa sun ziyarci Buharin, kuma sun sha dariya.
“A matsayina na Wazirin Adamawa, na tsaya domin gudanar da shagungulan Sallah a Adamawa, inda na wakilci Sarkin Adamawa, Lamiɗo Fombina a wasu shagulgulan.
“Yau kuma na kai ziyarar gaisuwar Sallah ga Muhammadu Buhari wanda ya shugabanci ƙasar a tsakanin 2025 zuwa 2023. Na ji daɗin ziyarar, saboda kamar yadda ya saba, ya yi ta ba mu dariya sai da haƙarƙarina suka yi zafi.”
Sai dai Atikun bai yi ƙarin haske kan ko akwai wani abu mai alaƙa da siyasa da suka tattauna da tsohon shugaban ƙasar ba a lokacin ziyarar.
A baya-bayan nan ƴansiyasa da manyan jami’an gwamnati na yawan kai wa tsohon shugaban ziyara tun bayan da ya koma gidansa na Kaduna daga Daura, inda ya shafe shekaru biyu tun bayan sauka daga mulki.