Hukumar kula da shige da fice NIS ta mayar da ‘yan kasar Mali su 62

Nigeria Immigration scaled

Hukumar kula da shige da fice ta ƙasa (NIS) reshen iyakar Illela da ke Jihar Sakkwato, ta tabbatar da mayar da ‘yan Jamhuriyar Mali su 62 zuwa gida ta hannun jami’an hukumar sa ke kan iyakar ta Illela.

Kwamandan hukumar Mista Tony Akuneme, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya kara da cewa mutanen sun hada da maza 51 da mata 11.

Akuneme ya ce tawagar jami’ai takwas karkashin jagorancin Mamoud Sadiq ne suka raka su a cikin bas guda biyu.

Ya ce tawagar ta isa kan iyakar ne da misalin karfe 8:00 na yammacin ranar Juma’a.

A wani labarin mai alaka da wannan, shugaban NIS ya ce ana ci gaba da aikin gina manyan gine-ginen da kuma kananan cibiyoyin da ake kira Forward Operating Bases (FOB) a ofishin kula da iyakar ta Illela.

Ya ce wannan mataki na cikin ƙudirin babbar Kwanturola janar ta NIS, Kemi Nandap, na ganin an kawar da ‘yan ci-rani a kasar nan a fadin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

Akuneme ya tabbatar wa da jama’a cewa al’amura sun lafa a yankunan Illela da Tangaza, inda sojoji da jami’an tsaro ke ci gaba da tunkarar barazanar ‘yan bindigar Lakurawa.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here