Buba Marwa ya kaddamar da barikin NDLEA da cibiyar gyaran hali

NDLEA Rehab 750x430

Shugaban hukumar NDLEA, Birgediya janar Mohammed Buba Marwa ya kaddamar da sabbin gidajen kwana da kuma cibiyar gyaran hali a jihar Kano.

A yayin kaddamar da bikin a ranar Asabar, Marwa ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu bisa ci gaba da goyon bayansa da jajircewarsa ga jami’an tsaro.

Ya bayyana cewa sabon barikin na da burin samar da kwanciyar hankali ga ma’aikata, tare da tabbatar da cewa iyalansu sun tsira yayin da suke bakin aiki.

Shugaban ya kuma yabawa hukumomin shiyya da na jiha da suka hada da rundunar MAKIA bisa kokarin da suke yi na dakile tu’ammali da miyagun kwayoyi.

Karanta: JAMB ta sanar da sabuwar ranar da za a rubuta UTME ta shekarar 2025

Jihar Kano ce ta biyu a yawan masu shan muggan kwayoyi, inda kashi 17 cikin 100 ke yaduwa a tsakanin mutane masu shekaru 15 zuwa 64.

“A cikin shekaru hudu da suka gabata, mun ba da shawarwari tare da gyara halayyar mutane 22,000 a fadin kasar,” in ji shi.

Marwa ya yi gargadin cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi na ci gaba da lalata rayuwar matasa, iyalai, da al’umma, inda ya bukaci daukar matakin hadin gwiwa kan lamarin.

Ya yi kira ga iyaye da su yi taka-tsan-tsan wajen gano shan miyagun kwayoyi a tsakanin yaransu, inda ya ba da shawarar su rika samun kayan gwajin daga ofisoshin NDLEA.

Ya bukaci shugabannin al’umma, sarakunan gargajiya, da malaman addini su marawa hukumar baya wajen yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi.

Shugaban hukumar ta NDLEA ya karfafa gwiwar jami’an su da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu na yaki da miyagun kwayoyi a fadin kasar nan.

Ya kuma tunatar da ma’aikatan da su kiyaye tsaftar sabbin bariki tare da tabbatar da kula da su yadda ya kamata. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here