Malamin wata makarantar Islamiya, wadda aka sace ɗalibanta a gonarsa a ƙarshen makon da ya gabata, Malam Aminu Bako, ya tabbatar da cewa ’yan bindiga sun tuntubi shugabannin ƙauye, inda suka nemi kuɗin fansa na sama da Naira miliyan 100 domin sakin ɗaliban.
Malam Bako ya kuma fitar da sunayen yaran da aka sace, tare da yin kira da a gaggauta ɗaukar matakin soji domin kuɓutar da su.
Sai dai ya koka da cewa makarantar da iyalan waɗanda aka sace ba su samu wani tallafi na zahiri ba domin ceto ɗaliban 15 tun bayan faruwar lamarin, in ban da ƙoƙarin ’yan sa-kai na yankin.
Bako ya shaida wa manema labarai cewa shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Rafi da Baturen ‘Yan sanda su kaɗai ne jami’an gwamnati da suka kai ziyara tun bayan faruwar lamarin.
A cewarsa, bayan ziyarar jami’an biyu, an bar mutanen yankin su dogara da ’yan sa-kai, waɗanda ke ƙoƙarin bin sawun masu garkuwar.
Malam Bako ya ce sabon bayanin da aka samu ta hanyar bayanan sirri na ’yan sa-kai ya nuna cewa har yanzu ana tsare da yaran a cikin jihar Neja, a wani keɓantaccen gini da ’yan bindiga masu ɗauke da manyan makamai ke gadinsa.
Ya jaddada cewa matakin soji ne kaɗai zai iya tabbatar da kuɓutar da su.
“Mun ji cewa har yanzu suna cikin jihar Neja, an kulle su a wani gini, mai yiwuwa ma ba tare da abinci ba. Muna cikin damuwa, muna son hukumomi su kawo mana ɗauki domin su kuɓutar da su,” in ji shi.
Malamin makarantar Islamiya ya ƙara bayyana cewa iyayen yaran suna matsa masa lamba sosai tun bayan sace ɗaliban, saboda a dabi’ance suna cikin fargaba game da lafiyar ’ya’yansu.
Ya ce ’yan bindigar sun tuntubi shugabannin ƙauye a daren da ya gabata, inda suka nemi kuɗin fansa na sama da naira miliyan 100.
Read also: Gwamnatin Kano ta rusa cibiyar kasuwanci ta jihar, ta kafa kwamitin riko
Wani mahaifi, Malam Adamu, shi ma ya tabbatar da cewa ’yan bindigar sun yi wannan buƙata ne saboda tun farko sun yi zaton ɗaliban na makarantun gwamnati ne, ba na makarantar Islamiya ba.
“Sun faɗa wa duk wanda ya yi magana da su jiya cewa ɗaliban na makarantun gwamnati ne, don haka a biya sama da naira miliyan 100, amma aka faɗa musu cewa ɗaliban makarantun Islamiya ne.”
Malam Adamu ya yi kira ga gwamnatin jihar Neja da ta shigo cikin lamarin tare da samar da tallafin tsaro.
“Wannan ba lokacin da za a bar mu da ’yan sa-kai kaɗai ba ne,” in ji shi.
Dangane da ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da kuɓutar da ɗaliban da aka sace, an kasa samun kwamishinan tsaron cikin gida, Justin Maurice Magaji, ta wayar tarho, saboda shi da sauran jami’ai suna halartar taron majalisar zartarwa ta jiha.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda (PPRO), SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar wa jaridar LEADERSHIP cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari ƙauyen Tungan Bako da ke ƙaramar hukumar Rafi, inda suka sace wasu mutane da ke aiki a gona.
Ya ce rahoton ’yan sanda ya nuna cewa kusan 14 daga cikin waɗanda aka sace ɗaliban makarantar Islamiya ne, waɗanda ke taimaka wa malaminsu wajen girbin masara a gonar.
Ya tabbatar da cewa haɗin gwiwar jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da ayyukan ceto waɗanda aka sace, duk da cewa mazauna ƙauyen sun bayyana cewa ’yan sa-kai ne kaɗai ke aikin a wurin.
Read also: Rikicin Siyasa: Gwamna Yusuf ya sasanta Barau da Abba Bichi
A halin da ake ciki, malamin Islamiyyar ya bayar da sunayen daliban da aka sace yayin da suke girbin masara a gonarsa kamar haka: Hassana Isah, Aliya Ahmad, Hajara Musa, Hauwa’u Abubakar, Halima Yahaya, Asma’u Jamilu, Radiya Salisu, Aminatu Salisu, Aisha Bello, Rahinatu Sani, Aminatu Alhassan, Nafisa Ayuba, Bilkisu Adamu da Salaha Abdullahi da kuma Hajara Salisu.













































