Ƙungiyar tsofaffin ma’aikata masu fensho ta kamfanonin NEPA da PHCN sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan hakkokin da aka rike musu tsawon fiye da shekaru 25.
Shugaban ƙungiyar, Mista Oladimeji Dunmoye, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Legas ranar Alhamis, inda ya ce tun bayan rushewar Kamfanin samar da hasken lantarki na (PHCN), tsofaffin ma’aikata sun shiga cikin matsanancin rayuwa.
Ya ce duk da alkawuran gwamnati da hukumomin da abin ya shafa, ba a warware batun jinkirin biyan hakkokin fansho ba.
Dunmoye ya zargi hukumar kula da tsarin fansho ta wucin gadi da hana biyan hakkokin tsofaffin ma’aikatan daga shekarar 2000 zuwa 2025, duk da cewa gwamnati ta samar da isassun kudade.
Ya bayyana cewa da dama daga cikin mambobinsu sun rasu suna jiran hakkinsu, yayin da wasu ke kasa samun kulawar lafiya.
Ya ce ƙungiyar ta rubuta wasiku akalla sau bakwai zuwa ga hukumar a Abuja amma aka yi biris da su, haka ma har zuwa fadar shugaban ƙasa an aika korafi sau uku tsakanin 2021 zuwa 2025 amma babu amsa.
A cewarsa, maimakon biyan hakkin ma’aikata, shugabannin hukumar suna gudanar da yaudararrun shirye-shiryen kafafen yada labarai tare da wasu jami’ai da shugabannin ƙungiyoyin ƙarya.
Karin labari: Tsofaffin Ƴan sanda na shirin yin zanga-zanga saboda matsalar Fansho
Ƙungiyar ta bukaci a biya dukkan bashi gaba ɗaya, a tabbatar da biyan fansho akai-akai, tare da girmama gudummawar da ma’aikatan lantarki suka bayar wajen gina ƙasa.
Dunmoye ya yi gargadin cewa za su ƙara kaimi wajen fafutuka har sai an tabbatar da adalci.
Shi ma Mista Julius Ayodeji, mai tsara ayyuka na biyu a ƙungiyar, ya ce kin biyan hakkoki ya jefa iyalan tsofaffin ma’aikatan cikin mawuyacin hali, yana mai kiran gwamnatin tarayya ta duba su a matsayin muhimman ‘yan ƙasa.
Ya nemi Majalisar Dokoki, ƙungiyoyin ƙwadago da kungiyoyin farar hula da su tallafa musu.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa a lokacin zanga-zangar, masu fanshon sun rike kwalaye masu taken “Ku biya mana hakkokinmu yanzu” da “Adalci ga tsofaffin ma’aikata.”
Babban matsayar taron ita ce ƙaddamar da ƙorafi ga Ma’aikatar Kuɗi da Hukumar Fansho (PenCom) domin kawo ɗauki cikin gaggawa.
NAN











































