Hukumar da da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta tabbatar da cewa gobarar da ta tashi a kasuwar Mandilas da ke tsibirin Legas ta lalata gine-gine guda huɗu tare da shaguna kusan 200.
Sanarwar hukumar da aka wallafa a shafinta na X ta bayyana cewa gobarar ta faru ne tsakanin ranar Talata da Laraba, 16 ga Satumba, sakamakon matsala daga wata na’urar canjin wuta a ɗaya daga cikin gine-ginen.
Rahotanni sun nuna cewa kasancewar kayayyaki masu saurin kamawa da wuta irin su kaya, takalma da robobi a cikin shagunan ya taimaka wajen bazuwar gobarar cikin sauri zuwa wasu gine-gine.
NEMA ta ce jami’an kashe gobara na tarayya da na Jihar Legas, tare da rundunar agajin gaggawa ta jihar da sauran masu ruwa da tsaki, sun isa wurin cikin gaggawa domin kashe gobarar.
Karanta: Hukumar tattara haraji ta ƙasa FIRS ta rasa manyan ma’aikata hudu sakamakon gobara a Legas
A cewar hukumar, haɗin kan waɗannan jami’ai ne ya taimaka wajen dakile gobarar da hana ta ƙara barna.
Sanarwar ta ƙara da cewa duk da tsananin gobarar, jami’ai sun yi aiki dare da rana har zuwa lokacin da aka kashe wutar gaba ɗaya.
Wani mutum ɗaya ne ya samu rauni sakamakon shakar hayaƙi, kuma an kai shi asibiti domin samun magani.
Rundunar ’yan sanda ta Najeriya ta kasance a wurin don tabbatar da tsaro da kuma hana barna ko sata.
Shugaban NEMA na yankin Legas ya yaba da jajircewar jami’an da suka halarci kashe gobarar, tare da tabbatar da cewa hukumar za ta tallafa wa ’yan kasuwar da abin ya shafa.
Ya kuma yi kira da a ƙara wayar da kai kan matakan tsaro, musamman a kasuwanni da ke da kayayyaki masu saurin kamawa da wuta.
Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomi domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a wuraren kasuwanci.
NAN












































