Shugaban kasa Bola Tinubu ya aike da ta’aziyyarsa ga iyalai da mabiya na fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Abubakar Giro Argungu wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Laraba.
Tinubu ya bayyana rasuwar shugaban addinin a matsayin rashi da ya wuce sauran al’ummar marigayin, a matsayin wanda ya shafi kasa baki daya, duba da irin gudunmawar da ya bayar ga kundin karatun addinin Musulunci.
Marigayin mai wa’azi ne a karkashin kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa’iqamatus Sunnah (JIBWIS).