Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar gwamna a jihar a shekarar 2023.
Malami wanda ya bayyana a gaban magoya bayan sa a jihar Kebbi ya yi alkawarin ba zai ci amana su ba.
“Idan Allah cikin rahamarSa ya sanya komai ya tafi daidai, ni a matsayina na dan siyasa zan tsaya takarar Gwamnan Jihar Kebbi, Ina neman goyon bayan ku.
“Ina so in sanar da cewa lallai zan tsaya takara kuma a don haka ina dogara ga addu’o’in ku da goyon bayan ku domin mu yi aiki ta hanyar da zamu tsira tare.
A cewar jaridar Thisday, Babban Lauyan Najeriya, ya yi nuni da cewa shugabanni na bukatar mabiya kuma mabiya su kuma suna bukatar shugabanninsu domin ganin ‘yan kasa sun amfana, kamar yadda ya yi alkawarin yin aiki ba dare ba rana domin juya rayuwar ‘yan kasa.
A baya dai Malami ya shaidawa abokansa na kusa aniyarsa ta tsayawa takarar zaben jihar Kebbi.
Tabbas zai tsaya takara a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma zai nemi ya gaji gwamna mai ci Abubakar Atiku Bagudu wanda ke kammala wa’adinsa na biyu.
A shekarar 2014, Malami ya sayi fom din tsayawa takarar gwamnan jihar Kebbi a karkashin jam’iyyar APC, amma ya sha kaye a hannun Bagudu a zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Shugaban kasa Buhari ya nada shi a matsayin babban lauyan Tarayya matsayin da yake yanzu tun daga shekarar 2015.
An haife shi a ranar 17 ga Afrilu 1967 a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi.
Malami ta samu shaidar kammala karatunta na farko (FSLC) a makarantar firamare ta Nassarawa, Birnin Kebbi. Ya wuce Kwalejin Fasaha da Nazarin Larabci don karatun Sakandare.
Ya samu digirin digirgir a fannin shari’a a Jami’ar Usmanu Danfodiyo a shekarar 1991 sannan aka kira shi Bar a 1992.
A shekarar 1994, Malami ya samu digiri na biyu a fannin harkokin gwamnati a jami’ar Maiduguri.
A shekarar 2011, Malami ya rike mukamin mai ba da shawara kan harkokin shari’a na jam’iyyar CPC, da shugaban kungiyar shari’a, kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa da kuma shugaban kungiyar lauyoyi na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na CPC.
Malami na daga cikin wadanda suka tsara ficewar jam’iyyar APC kuma mamba a kwamitin hadakar jam’iyyu na CPC, ACN, ANPP, bangaren APGA, DPP wajen kafa jam’iyyar APC.












































