Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), a ranar Juma’a da ta wallafa sunan Oladipupo Adebutu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamnan Jihar Ogun na shekarar 2027 cikin sa’o’i 24.
Mai shari’a Peter Lifu, a hukuncin da ya yanke, ya bayyana cewa INEC ba ta da ikon cire sunan ɗan takarar da wata jam’iyyar siyasa ta tsayar bisa ƙa’ida da kanta.
Read also: Yan sanda sun kama wani matashi dan shekara 20 da ya kashe mahaifinsa a Jigawa
Mai shari’ar ya ce matakin hukumar ya saɓa wa kundin tsarin mulki, ya saɓa wa doka kuma ba shi da wani tasiri na shari’a.
Mai Shari’a Lifu ya bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya ko kuma babbar kotun jiha ce kaɗai ke da ikon ayyana rashin ingancin takara, ba INEC ba.
Ya kuma ce hukumar ta tauye wa Adebutu haƙƙinsa na samun adalci ta hanyar sauraron ɓangarensa kafin yanke hukunci.
Alƙalin, wanda ya yi watsi da ƙin amincewa da ƙarar da INEC ta gabatar tun da farko, ya bayyana cewa ƙarar tana da inganci kuma kotu na da hurumin sauraron ta.
Read also: Ƴan jarida sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Bauchi
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa PDP da Adebutu sun shigar da ƙarar ne a ranar 22 ga Oktoba, bayan cire sunan Adebutu daga cikin jerin sunayen waɗanda ke takarar kujerar gwamnan Jihar Ogun.
Masu ƙarar sun maka INEC a matsayin wadda ake ƙara ita kaɗai, ta hannun lauyansu, Ahmed Raji, SAN.
Masu ƙarar, waɗanda suka gabatar da tambayoyi shida domin kotu ta tantance, sun kuma nemi kotun ta ba su wasu umarni guda 11.
Sun nemi kotun ta soke matakin hukumar na ƙin saka sunan Adebutu, cire shi ko kuma ƙin wallafa sunansa a jerin sunayen ƴan takarar ƙarshe da hukumar ta wallafa a ranar 10 ga Oktoba, bisa zargin tauye masa haƙƙin samun adalci da kuma saɓa wa tanade-tanaden sashe na 29 da na 32 na Dokar Zaɓe ta 2026.
Haka kuma, sun nemi kotun ta umarci INEC da ta saka ko wallafa sunan Adebutu cikin sa’o’i 24 da bayar da hukuncin a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP na gwamnan Jihar Ogun a zaɓen gama-gari na shekarar 2027, tare da wasu buƙatu.
Read also: Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi 3
(NAN)













































