Bayan Tanko, Mataimakin Sakataren Yaɗa Labaran NDC na Ƙasa ya fice daga jam’iyyar

NDC NDC

Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar NDC, Abdulmumin Abdulsalami, ya bar jam’iyyar, inda ya yi zargin rashin adalci, ware shi daga harkokin jam’iyyar da kuma katsalandan daga wasu manyan jami’anta a matsayin dalilan ficewarsa.

Abdulsalami ya sanar da matakin nasa ne a cikin wata wasiƙa da ya aikawa Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Moses Cleopas, ta hannun tsohon shugaban jam’iyyarsa na mazaba a Nagazi, ƙaramar hukumar Adavi da ke Jihar Kogi.

A cikin wasiƙar mai taken “Wasikar Murabus Daga Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress: Janyewa Daga Dukkan Alƙawura da Ayyukan Siyasa na Jam’iyyar”, ya ce ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ne bayan ya fahimci cewa gudunmawar da yake bayarwa ba ta dace da muradun wasu masu faɗa-a-ji a cikinta ba.

Ya kuma bayyana cewa yawan korafe-korafe kan abin da ya kira rashin adalci da kuma buƙatarsa ta kare kwanciyar hankalinsa na daga cikin dalilan da suka sa ya ɗauki matakin.

“A matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa jam’iyyar NDC, kana kuma jagora mai muhimmanci a lokacin kafuwarta, na ga ya zama dole in fice daga cikinta bisa radin kaina, bayan da na fahimci cewa kyakkyawar gudunmawar da na bayar wajen haɓaka jam’iyyar da nasarorinta ba ta dace da muradun wasu tsirarun jami’ai masu faɗa-a-ji waɗanda ke tafiyar da al’amuranta ba.

“Haka kuma, wannan mataki da na ɗauka bayan zurfafa tunani shi ne mafi alheri a gare ni, domin na fi son kare kwanciyar kaina maimakon ci gaba da korafe-korafe a duk lokacin da na ga irin rashin adalcin da ake yi mini.”

Abdulsalami ya taɓa riƙe muƙamin shugaban riƙon ƙwarya na NDC a Jihar Kogi kafin daga bisani ya zama Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa, sannan daga baya Mataimakin Daraktan Ƙasa mai kula da ayyuka da farar hula.

Ya gode wa jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Henry Dickson, bisa damar da ya ba shi, tare da jinjinawa abokan aikinsa, masu fafutukar ƙungiyoyin farar hula da kuma ’yan jarida da suka yi aiki tare da shi a lokacin da ake kafa jam’iyyar.

Murabus ɗin Abdulsalami na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun saɓani kan iko da tsarin tafiyar da jam’iyyar NDC, wadda ta wanzu tun kafin shigowar ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi da mataimakinsa, Rabiu Musa Kwankwaso.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here