Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da fashi da makami, waɗanda ake zargin suna addabar dajin Falgore da al’ummomin da ke makwabtaka da shi a Ƙaramar Hukumar Doguwa, inda aka ƙwato kuɗi Naira 600,000, wayoyin hannu guda tara da wasu kayayyakin da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata laifuka.
Rundunar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kakakinta, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar Talata, 10 ga watan Nuwamban 2026, inda ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a ranar 6 ga watan Nuwamba, bayan jami’an sashen ’yan sanda na Doguwa sun samu sahihan bayanan sirri.
Read also: Gwamnatin Jigawa zata Kashe biliyan 1.4 domin gyaran Makabartu da Masallatai
SolaceBase ta rawaito cewa waɗanda aka kama sun haɗa da Sulaiman Alhaji Umaru, mai shekaru 35, daga ƙauyen Damau da ke Ƙaramar Hukumar Kubau a Jihar Kaduna da Abubakar Sale, mai shekaru 22, daga Ƙaramar Hukumar Gwarzo a Jihar Kano.
A cewar rundunar ’yan sandan, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, Sulaiman, ya amsa cewa ya haɗa kai da wasu mutum bakwai wajen yi wa Adamu Sa’adu, ɗan Kubau a Jihar Kaduna, fashi tare da ƙwace masa kuɗi Naira miliyan 1.35 da wasu kayayyaki a yankin dajin Falgore.
’Yan sandan sun ce sun ƙwato kuɗi Naira 600,000, wayoyin hannu guda tara masu nau’o’i daban-daban, wuƙaƙe da kuma sanduna daga hannun waɗanda ake zargin.
Read also: Anga watan Ramadana a Najeriya – Sarkin Musulmi
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an sashen Doguwa bisa nasarar gudanar da aikin, inda ya danganta nasarar da sahihan bayanan sirri, gaggawar ɗaukar mataki da haɗin kan al’umma.
Bakori ya kuma sake jaddada aniyar rundunar na ci gaba da amfani da bayanan sirri wajen yaƙi da aikata laifuka da gudanar da ayyukan tsaro, bisa tsarin aikin sufeto-janar na ’yan sanda, IGP Olatunji Rilwan Disu.
Ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar za ta ci gaba da tabbatar da tsaro, tare da kare rayuka da dukiyoyinsu a faɗin jihar.
Haka kuma, rundunar ta bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin cafke sauran mambobin ƙungiyar da suka tsere, yayin da bincike kan lamarin ke ci gaba da gudana.
Read also: Mafi Karancin Albashi: Gwamnatin tarayya ta sake gayyatar kungiyar kwadago
Ta ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.












































