Gwamnatin Kano ta amince da sama da Naira biliyan 2.65 don gyaran bututun ruwa da faɗaɗa su

Governor Abba Kabir Yusuf 640x430 (2)

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe sama da Naira biliyan 2.65 domin kula da bututun ruwa, gyara, faɗaɗa su da kuma sauya musu wurare a faɗin jihar, domin inganta samar da ruwan sha mai tsafta ga al’umma.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon taron Majalisar Zartarwa ta Jiha da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano.

Bature ya ce an amince da kuɗaɗen ne bayan tattaunawa kan batutuwan da suka shafi Ma’aikatar Albarkatun Ruwa a yayin zaman majalisar.

Kwamishinan ya bayyana cewa za a yi amfani da kuɗaɗen wajen magance matsalolin kula da bututun ruwa da gyaransu, tare da faɗaɗa hanyoyin sadarwar bututun da ake da su da kuma sauya wuraren da suke domin inganta rarraba ruwa.

Ya ce wannan mataki na da nufin tabbatar da samar da ruwan sha mai tsafta cikin daidaito ga al’ummomi a faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa majalisar ta fahimci cewa ya zama wajibi a ɗauki wannan mataki domin ƙarfafa kayayyakin aikkn .samar da ruwa da kuma magance matsalolin da ke kawo cikas ga rarraba ruwa ga mazauna jihar.

A cewarsa, wannan amincewa na daga cikin shawarwarin da majalisar ta cimma yayin taronta na musamman da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta.

Taron ya kuma tattauna kan kasafin kuɗin shekarar 2027 da kuma ƙudirin gwamnatin jihar na biyan bashin haƙƙoƙin fansho da ake bin ta, wanda aka kiyasta ya kai Naira biliyan 42, tsakanin watan Nuwamba na 2026 zuwa watan Afrilun 2027.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here