Gwamnatin Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na watan Maris

Abba Kabir Yusuf Kano Kano 715x430

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na karshen watan Maris wanda ta shirya gudanarwa ranar Asabar.

Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar, Dakta Dahir Muhammad Hashim ne ya sanar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafin sa na sada zumunta ranar Alhamis.

Karin karatu: Gwamnatin Kano ta yi haɗin gwiwa da kamfanin Aqua Power don sarrafa shara da samar da makamashi

Sanarwar ta ce an dakatar da aikin tsaftar muhallin ne domin baiwa mazauna Kano damar shirye-shiryen bukukuwan Sallah karama.

Ya kara da cewa “An bar jama’a su fita su ci gaba da shirye-shiryensu na Idi, amma muna karfafa wa kowa gwiwa da ya tsaftace muhallinsa domin tabbatar da cewa mun gudanar da bukukuwan Idi a cikin tsaftataccen muhalli.”

Dakta Hashim ya kuma bayyana cewa za a ci gaba da tsaftace kasuwanni da ofisoshi kamar yadda aka saba a ranar Juma’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here