Gwamnatin Kano ta gargadi masu zubar da shara barkatai, ta lashi takobin daukar mataki

IMG 1286

 

Hukumar Kula da Shara da Tsaftar Muhalli ta Kano (REMASAB) ta kaddamar da gagarumin aiki na kwashe shara a guraren da aka zubar ba bisa ka’ida ba a Shataletalen Hajj Camp da Gadar Indomie da ke kan Titin Airport.

SolaceBase ta ruwaito cewa hukumar ta hana zubar da shara a yankin baki daya, lamarin da ya kawo karshen sama da shekaru 15 na zubda shara barkatai a yankunan, wanda ke haddasa ambaliya, gurbata muhalli, da yaduwar cututtuka.

Yayin jagorantar aikin tsaftace yankin a ranar Alhamis, Mataimakin Babban Daraktan REMASAB, Lamin Mukhtar Hassan, ya bayyana wuraren zubar da sharan a matsayin barazana babba ga lafiyar jama’a da muhalli.

Hassan ya ce, “Wadannan magudanan ruwa na hade da sauran da ke cikin birnin Kano, kuma idan an toshe su da shara, hakan na haddasa ambaliya a cikin gari.”

Ya kara da cewa, “Sharar da ake zubarwa akan hanya babba yana bata kyawun birnin, musamman a idon baki da ke shigowa.”

Domin farfado da yankin, REMASAB na shirin cike wuraren da aka share da yashi tare da ba wa masu saida furanni da bishiyoyi don inganta iska da kara kyawun birnin.

Hukumar ta kuma bayyana shirinta na tallafawa masu tara shara ta hanyar samar musu da damammakin zuba jari don dogaro da kai mai dorewa.

An gargadi jama’a da su daina zubar da shara barkatai kuma su yi amfani da wuraren tara shara da gwamnati ta tanada.

“Gwamnati ta samar da ingantattun wuraren zubar da shara, kuma koyaushe muna shirye don kwashe shara daga wuraren da aka tanada. Tsabtace Kano hakki ne na kowa da kowa,” in ji jami’in.

Da wannan matakin, REMASAB na aikawa da sako karara cewa ba za a lamunci zubar da shara ba bisa ka’ida ba.

Sauya fasalin wadannan wurare yana nufin sabon salo a kokarin tsaftace Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here