Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya rantsar da sababbin kwamishinonin sa yau Juma’a.
Jaridar solacebase ta rawaitu cewa kwamishinoni da majalisar dokokin jihar ta tan-tan ce zasu maye gurbin wadan da suka ajiye aikin su domin shiga zaben 2023.
Bikin rantsuwar ya gudana ne a filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata.
Yayin rantsar dasu Ganduje ya ce ya nada kwamishinonin ne bisa dacewa da kuma kwarewa.
Sababbin kwashinonin da aka rantsar sune Dan azumi Gwarzo, Abdulhalim Dan Malik, Lamin Sani Zawiya, da kuma Ya’u Yanshana.
Sauran sun hada da Garba Yusuf, Dakta Yusuf JY Rurum, Saleh Kausani, Ali Musa Hamza Burn Burn, Alh Kabiru Muhammad sai kuma Adamu Abdul Panda.













































