Zargin almundahana: EFCC zata daukaka kara kan hukuncin da aka yi Jonah Jang da Pam

Jonah Jang 750x430 1
Jonah Jang 750x430 1

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Kasa Ta’annati (EFCC),ta yi martani kan hukuncin da wata kotu ta yanke, wadda ta kori kara tare da wanke tsohon Gwamnan Jihar Filato, Jonah David Jang, bisa zargin cin hanci da rashawa.

Kotun ta kuma wanke tsohon mai karbar kudi na ofishin sakataren gwamnatin jihar, OSSG, Yusuf Pam.

Shugaban sashen yada labaran hukumar EFCC Wilson Uwujaren, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a,Inda ya Kara da cewa hukumar ta fara gudanar da shirye-shiryen daukaka kara Kan hukuncin da kotun ta yi.

Uwujaren ya ce “An jawo hankalin hukumar ta EFCC, kan hukuncin da Mai shari’a C.L Dabup na Babbar kotun Jihar Plateau ya yanke a ranar Juma’a, 2 ga watan Satumbar Shekarar 2022, inda ta sallami tsohon gwamnan jihar Filato , Sanata Jonah David Jang tare da wanke shi, shi da tsohon mai karbar kudi na ofishin sakataren gwamnatin jihar, OSSG, Yusuf Pam, bisa tuhume-tuhume goma sha bakwai da suka shafi zamba cikin aminci da karkatar da kudaden jihar Filato har Naira biliyan 6 da miliyan dari 3.” A cewar hukumar EFCC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here