Jam’iyyar ADC ta dakatar da dan takararta na shugaban kasa, Dumebi Kachikwu, daga jam’iyyar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar nq Kasa Dakta Bamidele Ajadi, ya Sanya hannu a ranar asabar.
Jam’iyyar ta zargi Kachikwu da wasu laifuka wadanda suka sabawa dokokin Jam’iyyar.
Sanarwar ta bayyana cewa an dauki matakin ne bayan wani taron gaggawa na Kwamitin kolin jamiyya da aka gudanar a ranar Juma’a, 2 ga Satumbar Shekarar 2022.
Jam’iyyar ta bayyana cewa ta dauki matakin ne akan Kachikwu, sakamakon wasu ayyuka dake nuna “cikakkiyar rashin da’a da badakala da batanci wadanda duka wadannan laifuka ne da wanda ke son zama shugaban Najeriya bai kamata ya aikata su ba.”
Jam’iyyar ta yi nuni da cewa, a baya ya taba yin wasu kalamai da nufin bata wa mambobin Jam’iyyar ta ADC na kasa baki daya, wanda kwamitin kolin ta yi watsi da su, domin a samu zaman lafiya.













































