NAFDAC ta lalata kayayyakin jabu da abinci na sama da Naira biliyan 120  

NAFDAC destroys 750x430

 

Hukumar NAFDAC ta yi nasarar lalata magunguna, kayan abinci, da kayan sha na jabu da suka kai darajar sama da Naira biliyan 120 tsakanin Oktoba zuwa Disamba 2024.

Shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce za a dauki mataki mai tsauri kan masu kawo hadari ga lafiyar ‘yan kasa ta hanyar rarraba kayan jabu.

NAFDAC ta kai samame a kasuwanni da manyan shaguna a jihohi da dama, ciki har da Legas, Abuja, Kaduna, da Aba.

Hukumar ta lalata magunguna marasa rajista na Naira biliyan 11 a Ibadan da shinkafar jabu ta Naira biliyan 5 a Abuja da Nasarawa.

Farfesa Adeyeye ta gargadi jama’a da su rika siyan kayan da ke da lambar rajista ta NAFDAC daga wuraren da ake iya gane su, tana mai tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da kawar da kayayyakin da za su iya cutar da lafiyar al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here