NDLEA ta kama wani dan kasuwa da ya hadiyi kwayoyin hiroyin da koken 74 a filin jirgin Abuja

Suspected drug trafficker intercepted by NDLEA operatives at Abuja Airport 750x430

 

Jami’an Hukumar Dakile Shan Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) sun kama wani dan kasuwa mai shekaru 48, Ifeanyi Orizu, da ya sha kwayoyin heroin da cocaine 74.

A cewar mai magana da yawun NDLEA, Mr. Femi Babafemi, Orizu an kama shi ne yayin da yake kokarin shiga jirgin Air France 844 daga filin jirgin Nnamdi Azikiwe na Abuja zuwa Paris, Faransa, a ranar Lahadi, 22 ga Disamba.

Orizu ya ce yana da shago a Kasuwar Balogun da ke Lagos inda yake sayar da jakunkuna na makaranta kuma an yi masa alkawarin samun Euro 3,000 idan ya kai kayan zuwa Paris.

Hakazalika jami’an na NDLEA sun kwace jiragen ruwa guda biyu da aka cika da Cannabis a Eleko Beach da ke Lekki, Lagos, a ranar Kirsimeti.

Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba wa jami’an hukumar saboda kokarinsu da suka yi, yana mai kira ga su ci gaba da zage dantse wajen dakile sha da fataucin miyagun kwayoyi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here