An sace tsabar kudi naira miliyan 31 a gidan gwamnatin jihar Katsina

Naira bundle 1
Naira bundle 1

Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da sace miliyoyin kudi daga asusun gidan gwamnatin jihar, wanda har yanzu ba’a kai ga gano wanda yai satar ba.

Mai taimakawa gwamnan jihar kan Kafafan sada zumunta na zamani, Alhaji Al-Amin Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Alhamis.

Duk da cewa dai bai fadi adadin kudin da aka sace ba, ya ce dai anan ana binkice kan wa dan da ake zargi suna da hannu wajan satar.

Sai dai wani wanda baya so a bayyana sunan sa, ya shaidawa gidan TV na channel cewa kudin da aka sace sun kai kimanin naira miliyan 31.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here