Gwamna Nyesom Wike ya na karar ‘dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da kuma Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.
Nyesom Wike da wani jagora a PDP, Newgent Ekamon suka shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/782/2022 a game da rikicin takaran 2023. Gazette tace Wike da Newgent Ekamon su na tuhumar jam’iyyar PDP, hukumar INEC, Aminu Tambuwal da Atiku Abubakar a kan zaben tsaida gwani.
A karar da aka shigar, Wike da abokin kararsa sun nemi kotu ta raba gardama ko kuri’un Tambuwal za su iya komawa wajen Atiku a zaben na PDP.
Lauyoyin da suka kai kara sun nemi Alkali ya yi fashin baki kan makomar kuri’un Tambuwal, ganin ya janye takara a lokacin da an fara kada kuri’a.
Rahoton da aka fitar yace Lauyoyi na rokon kotu ta ruguza nasarar da Atiku Abubakar ya samu, idan ta tabbata Tambuwal ya fita daga takarar.
Masu karar sun kuma nemi hukumar INEC ta cire sunan Atiku Abubakar daga cikin ‘yan takara. A karshe, an roki kotun tarayyar ta tsaida Nyesom Wike a matsayin wanda ya lashe zaben gwani na shiga takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa da za ayi.












































