Gwamnatin katsina ta bude shafinta na yanar gizo domin masu sha’awar shiga gasar nuna baiwa ta KNTHC

Katsina opens portal for national talent hunt challenge
Katsina opens portal for national talent hunt challenge

Gwamnatin jihar katsina ta ce ta budi shafin ta na yanar gizo domin ‘yan asalin jihar da suke da sha’awar shiga gasar nuna baiwa ta kasa wato KNTHC.

Alhaji Ahmad Mansur-Kurfi, wanda shine yake shugabantar gasar ne ya bayyana hakan ranar Alhmais a Katsina, ya ce za’a raba fama-famai a duk kanan hukumomin jihar, sa boda masu sha’awa su nema.

Ya ce an shirya gasar ne domin karfafawa matasan da suke da baiwa domin su kara hazaka kan baiwar da Allah yai musu.

Ya kara da cewa gasar zata kasan ce rukuni uku, wadan da suka hada da bangaran fasahar zamani ICT, kida tare da wakoki da kuma harkokin kirkire-kerkire.

Ya kuma ja hankalin matasa da suyi anfani da wannan damar domin taimakon kansu da kuma ‘yan uwan su.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here