Gwamna Yusuf ya gabatar da kasafin kuɗi na 2027 na Naira tiriliyan 1.107, ya ware kashi 63 cikin 100 ga ayyukan raya ƙasa

Abba Kabir Yusuf Budget 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da ƙudiriin kasafin kuɗin Naira tiriliyan 1.107 na shekarar 2027 ga Majalisar Dokokin Jihar Kano, inda aka fi mayar da hankali kan ayyukan raya ƙasa, kammala ayyukan da ake gudanarwa da kuma bunƙasa yankunan karkara cikin gaggawa.

Kasafin kuɗin mai taken “Kasafin Kuɗin Ƙarfafa Nasarorin da Aka Samu Da Kuma Gaggauta Bunƙasa Yankunan Karkara”, ya kai jimillar Naira tiriliyan 1,107,024,004,244.48, kuma shi ne kasafin kuɗi na huɗu kuma na ƙarshe a zangon farko na gwamnatin.

Yayin gabatar da kasafin, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa an tsara shi ne domin ƙarfafa nasarorin da aka samu tun daga shekarar 2023, kammala muhimman ayyukan raya ƙasa da kuma inganta muhimman ayyukan jin daɗin al’umma kafin ƙarshen zangon farko na gwamnatin a ranar 29 ga watan Mayun 2027.

Ƙudirin kasafin ya ware Naira biliyan 693.47, kwatankwacin kashi 63 cikin 100, domin gudanar da ayyukan raya ƙasa, yayin da aka ware Naira biliyan 413.55, wato kashi 37 cikin 100, domin gudanar da ayyukan yau da kullum na gwamnati.

Gwamnan ya ce yadda aka fi ware kuɗaɗe ga ayyukan raya ƙasa na nuna ƙudurin gwamnatinsa na faɗaɗa ababen more rayuwa, bunƙasa rayuwar ɗan Adam da kuma zuba jari a fannonin da za su taimaka wajen haɓaka tattalin arzikin jihar.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati na sa ran samun Naira biliyan 692.64 a matsayin kuɗaɗen shiga na yau da kullum a shekarar 2027, waɗanda suka haɗa da Naira biliyan 142.84 daga kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR) da kuma Naira biliyan 549.80 daga asusun tarayya.

Gwamna Yusuf ya ƙara da cewa an samu nasarar aiwatar da sama da kashi 90 cikin 100 na shirye-shirye, ayyuka da manufofin da ke cikin kundin tsarin bunƙasa jihar na gwamnatinsa.

Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ƙara ƙaimi wajen sa ido kan aiwatar da kasafin kuɗin, tabbatar da gaskiya da riƙon amana domin ganin an gudanar da ayyukan yadda ya kamata tare da samun sakamakon da ya dace da kuɗaɗen da aka kashe.

Daga nan ne gwamnan ya miƙa ƙudirin dokar kasafin kuɗin shekarar 2027 ga Majalisar Dokokin Jihar domin nazari da kuma amincewa da shi.

Sanarwa daga:

Sunusi Bature Dawakin Tofa Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here