Badakalar N37bn: EFCC Ta Gayyaci Tsohuwar Ministar Buhari

EFCC

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gayyaci tsohuwar ministar harkokin jin kai, kula da bala’o’i, da ci gaban jama’a, Sadiya Umar-Farouq, kan ci gaba da binciken N37,170,855,753.44 da ake zargin ta karkatar da ta hannun wani dan kwangila, James Okwete. .

An bukaci tsohuwar ministar da ta bayyana a gaban masu bincike a hedikwatar EFCC, Jabi, Abuja a ranar Laraba, 3 ga watan Janairu, 2024, domin ta yi bayani kan zargin.

Takardar ta kara da wani bangare cewa, “Hukumar na binciken wani lamari ne da ya shafi karkatar da kudade da ya shafi ma’aikatar kula da jin kai da bala’o’i da ci gaban al’umma a lokacin da kike minista.

An kasa samun tsohuwar ministar domin jin ta bakinta a ranar Asabar din da ta gabata saboda wayar ta ta nuna cewa a kashe take. A lokacin da wakilinmu ya tuntubi tsohon mai taimaka mata kan harkokin labarai, Nneka Ikem kan lamarin, ya shaida wa wakilinmu a kashe wayarta take.

“Kamar yadda kake tambayata? Zan tambaye ka, a ina ka samu labarin cewa EFCC ta gayyace ta, “Ikem ya tambaya kafin ya kimtse kiran. Kiraye-kirayen da aka yi ya nuna wayarta a kashe.

A baya Umar-Farouq ta musanta sanin dan kwangilar, James Okwete, wanda har yanzu yana hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa.

Tsohuwar ministar ta wallafa a shafinta na twitter a ranar Litinin cewa, “An samu rahotanni da dama da ke alakanta ni da wani bincike da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta yi kan ayyukan wani James Okwete, wanda ban san ni ba.

Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya ki cewa komi kan gayyatar da akewa tsohuwar ministar a lokacin da Sunday PUNCH ta tuntube shi.

“Ba ni kusa a halin yanzu, kuma ba zan iya magana a kan hakan ba, don Allah,” in ji Oyewale.

A baya Sunday PUNCH ta bada rahoto cewa hukumar EFCC ta kama Okwete kan binciken da ake yi na N37.1bn da ake zargin ma’aikatar karkashin Umar-Farouq ta karkata.

Wannan ci gaban ya zo daidai da ake shirin fara binciken wasu ministoci uku, wadanda suka yi aiki a karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa zargin almundahana da aka kiyasta kimanin N150bn.

A baya majiya mai tushe ta tabbatarwa da jaridar Sunday PUNCH cewa Okwete yana bada hadin kai ga masu binciken.

Wasu daga cikin takardun sun bayyana cewa, bayan samun kudaden, Okwete ya mikawa ma’aikatan ofishin ‘yan canji ‘Bureau De Change’ N6,746,034,000, sannan ya ciro naira miliyan 540, ya siyo motoci na alfarma da naira 288,348,600 sannan ya sayi gidaje na alfarma a Abuja da jihar Enugu da N2,195,115,000.

Kamfanoni 53 ne aka rawaito an gano Okwete, wanda kuma aka ce sun yi amfani da kamfanoni 47 na kamfanonin wajen samun kwangilar Gwamnatin Tarayya da ta kai ta N27,423,824,339.86.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here