An biya ni naira Dubu Ɗari domin tayar da Bom a masallacin Maiduguri – wanda ake zargi

Ibrahim Mohammed

Wani da ake zargin mamba ne na ƙungiyar Boko Haram da aka kama dangane da harin bam da aka kai a wani masallaci a Maiduguri, jihar Borno, mai suna Ibrahim Muhammad ya bayyana cewa an ba shi kimanin Naira Dubu Ɗari domin aiwatar da harin.

Harin ya faru ne a ranar 24 ga watan Disamba, 2025, a masallacin da ke kasuwar Gamboru, lamarin da ya hallaka mutane 5 tare da jikkata 32, yayin da jama’a ke cikin ibada, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici da tashin hankali.

Wanda ake zargin, na daga cikin mutane biyu da sojoji suka kama, ya bayyana cewa shugabanninsa ne suka tura shi domin aiwatar da harin, kuma an tsara harin ne bisa umarnin manyan jagororin Boko Haram da ke aiki tsakanin jihar Adamawa da yankin tsaunukan Mandara inda ya bayyana sunayen su da Adamu da Abubakar.

A cewar shafin Zagazola Makama, wani dandali na yaƙi da ta’addanci, ya ce wanda ake zargi Ibrahim Muhammad ya bayyana cewa sun shiga masallacin ne bayan sallar azahar da la’asar, a lokacin da masallacin bai cika da mutane ba, suka nuna kamar masu ibada, inda abokin aikinsa ya fara tono rami domin dasa bam a tsakiyar masallacin, shi kuma yana tono rami a gefe.

A cewar sa, bayan tayar da bam ɗin, ya koma wurin da lamarin ya faru, inda ya yi kamar yana taimakawa wajen ceto mutane, yana ɗaukar gawarwaki da kuma wadanda suka jikkata zuwa motocin gaggawa, domin kada a gano rawarsa a harin.

Daga baya ya bayyana cewa ya wuce jihar Yobe domin wasu ayyuka, ciki har da leƙen asiri kan wuraren sojoji da ƙungiyoyin farauta domin kai hare-hare a gaba.

Ya ce ana biyansa tsakanin Naira Dubu Saba’in zuwa Dubu Ɗari a kowace manufa da ya aiwatar.

Binciken tsaro ya nuna cewa yana cikin wata babbar ƙungiyar ‘yan ta’adda da ke shirin kai hare-hare a sassan arewa maso gabas, karkashin rassan Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad, Ansaru da Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin.

An kama shi ne a Damaturu bayan farautar hadin gwiwa tsakanin mafarauta da dakarun Operation Hadin Kai, bayan da aka fara zarginsa saboda shigarsa cikin almajirai ba tare da dalili mai gamsarwa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here