Kananan hukumomi zasu fara karbar kason kudadensu kai tsaye karshen watan Janairu – Fadar Shugaban Kasa

Bola Tinubu Tinubu sabo 750x430

Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa daga karshen watan Janairu, kananan hukumomi a fadin Najeriya za su fara karbar kason kudadensu kai tsaye daga kwamitin asusun bai daya na gwamnatin tarayya (FAAC), wanda ke nuna wani gagarumin mataki na cin gashin kan kananan hukumomi.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa Sunday Dare ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da gidan talabijin na Arise News a daren ranar Alhamis.

Ya nanata kudurin Shugaba Bola Tinubu na aiwatar da hukuncin Kotun Koli na Yuli 2024, wanda ya ayyana ikon da jihohi kan kudaden kananan hukumomi ya sabawa tsarin mulki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here