Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Kimanin daraktoci 40 ne suka fadi jarrabawar cancantar nadin mukaman sakatarorin dindindin.
Wanda hakan ke nuna daraktoci 92 ne aka jera don zana jarrabawar da aka yi ranar 27 ga watan Mayu, 2024.
Yayin da daraktoci 40 suka samu kasa da kashi 50 cikin 100, wanda hakan ke nuna gazawa, kamar yadda sakamakon jarrabawar da aka fitar a Abuja, uku ba su halarta ba, yayin da darakta daya ya kasa kammala jarrabawar.
Karin labari: Kotu ta ba da umarnin kwace dala miliyan 1.4 da ke da alaka da Emefiele
Memo na watan Mayu 28, 2024 daga Ofishin Shugaban Ma’aikata mai alamar, “HCSF/CMO/AOD/012/IX/59′ ya lura cewa gwaji na gaba zai kasance gwajin tushen ICT.
An bayyana cewa, tun farko gwamnatin tarayya ta ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati ta sanar da fara aikin nadin sabbin sakatarorin dindindin da za su cike guraben da ake da su a Akwa Ibom da Anambra da Bauchi da Ebonyi da Jigawa da jihohin Ondo da Zamfara da Kudu maso Gabas da kuma shiyyar Kudu maso Kudu.
Karin labari: Tinubu ya saukakawa matafiya a tsarin sufurin jiragen kasa na Abuja zuwa Disamba
Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya Folashade Yemi-Esan ce ta bayyana hakan a wata takardar da ta aike wa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila da sakataren gwamnatin tarayya George Akume da dai sauransu.
A cikin sanarwar, wacce ita da kanta ta sanya wa hannu, Yemi-Esan ta lura cewa daraktocin da suka sami mukamin babban darakta a ranar 1 ga watan Janairu, 2022 ne kawai za a yi la’akari da su a cikin aikin.
Takardar ta kuma bayyana cewa, an cire jami’an da ke fuskantar ladabtarwa daga aikin.