Kotu ta ba da umarnin kwace dala miliyan 1.4 da ke da alaka da Emefiele

Kotu, umarnin, kwace dala, miliyan, alaka, Emefiele
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta sake bayar da umarnin kwace wasu makudan kudade Dala Miliyan 1.4 na wucin gadi da aka alakanta da tsohon...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta sake bayar da umarnin kwace wasu makudan kudade Dala Miliyan 1.4 na wucin gadi da aka alakanta da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Mai shari’a Ayokunle Faji ya bayar da umarnin a kwace kudaden ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Karin labari: Babban alkalin alkalan Najeriya ya gayyaci manyan alkalai kan hukunce-hukuncen masarautar Kano

Alkalin ya kuma umarci hukumar EFCC da ta buga wannan kudiri na wucin gadi a wata jarida ta kasa domin duk mai sha’awar kudin da ake nema ya bayyana a gaban Kotu tare da nuna dalilinsa cikin kwanaki 14 da ya sa ba zai zama na karshe na kwace wadannan kudaden.

Karin labari: Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin maido da tsohuwar waka a matsayin doka

Kotun ta bayar da wadannan umarni na sama ne a lokacin da ta ke ba da takardar bukatar da lauyan EFCC, Bilkisu Buhari-Bala ya mika.

An ce kudaden da aka yi hasashe a cikin asusun Donatone Limited suna cikin asusun Titan Bank Limited.

Karin labari: Babban sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya ya nada sabon sakataren rundunar na kasa da kasa

Mai shari’a Faji ya dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Yuni domin jin yadda aka yi watsi da kudaden.

A ranar 23 ga watan Mayu mai shari’a Yellim Bogoro na wannan kotun ya bayar da umarnin a kwace wasu kudade na wucin gadi da wasu kadarori da dama da suke da alaka da tsohon gwamnan babban bankin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here