Babban alkalin alkalan Najeriya ya gayyaci manyan alkalai kan hukunce-hukuncen masarautar Kano

Justice, Olukayode Ariwoola, babban, alkalin, alkalan, najeriya, jihar, kano, masarauta, hukunce-hukunce
Babban Alkalin Alkalan Najeriya (CJN), Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ya gayyaci babban alkalin babbar kotun tarayya, da kuma alkalin babbar kotun jihar...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Babban Alkalin Alkalan Najeriya (CJN), Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ya gayyaci babban alkalin babbar kotun tarayya, da kuma alkalin babbar kotun jihar Kano bisa wasu hukunce-hukuncen wucin gadi da suka saba wa masarautar Kano, lamarin da ya haifar da rashin tabbas a jihar.

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, karkashin Mai Shari’a S. A. Amobeda, ta bayar da umarnin korar Sarki Muhammadu Sanusi II daga Fadar Kofar Kudu, tare da karfafa ikon Sarkin Fulanin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Karin labari: Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin maido da tsohuwar waka a matsayin doka

“An ba da umarnin wucin gadi da ke hana wadanda ake kara gayyata, kamawa, tsarewa, barazana, tsoratarwa, musgunawa mai kara, ko tauye hakkinsa,” in ji Mai shari’a Amobeda.

Ya kara da cewa, “Wannan umarni ya tabbatar da cewa sarki Aminu Ado Bayero ya samu duk wani hakki da gata da aka same shi ta hanyar matsayinsa.”

A daya hannun kuma, babbar kotun jihar Kano a karkashin mai shari’a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin kare Muhammadu Sunusi da sauran manyan mutane daga cin zarafin da hukumomin jihar ke yi musu.

Karin labari: Buhari ya roƙi ‘yan Najeriya su sakawa gwamnatin Tinubu albarka

Wannan odar ta hana duk wani tsangwama ga ‘yancin cin gashin kan sarki da kuma kwace manyan alamomin ikonsa, kamar tagwayen mashi, hular sarauta ta Dabo, da takalman gashin jimina.

Mai shari’a Aliyu ya jaddada cewa, “An ba da umarnin na wucin gadi da zai hana wadanda ake kara zage-zage ko tsoratar da masu bukatar ko kuma kwace duk wata alama ta ikon Sarki.”

Ta kara da cewa, “An umurci wadanda ake kara da su ci gaba da kasancewa a halin da ake ciki har zuwa lokacin da za a saurari karar da kuma yanke hukunci a kan sanarwar.”

Karin labari: Babban sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya ya nada sabon sakataren rundunar na kasa da kasa

Waɗannan umarni masu karo da juna sun haifar da ruɗani game da haƙƙin sarakuna da kuma kare martabar sarakuna a Kano.

A ranar 13 ga watan Yuni ne za a ci gaba da sauraren karar babbar kotun jihar, yayin da babbar kotun tarayya ta dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Yuni.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here