Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa a yanzu fasinjoji za su iya tafiya kyauta a sabon tsarin sufurin jiragen kasa na Abuja har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a yayin da yake kaddamar da aikin gina layin dogo a Abuja domin cika shekara guda a kan karagar mulki.
Karin labari: Kotu ta ba da umarnin kwace dala miliyan 1.4 da ke da alaka da Emefiele
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nysom Wike, a wani taron manema labarai na ministar, ya ce layin dogo na Abuja zai yi aiki na tsawon watanni biyu kyauta daga ranar Talata.
Sai dai shugaban ya roki ministan da ya tsawaita tafiye-tafiyen kyauta domin mazauna yankin su samu damar yin bukukuwa.