Ya Zama Wajibi A Hukunta Wike – Dan Takarar Gwamna Ya Gayawa PDP

FB IMG 1703980975961 1 746x430

Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP, Alhaji Sadik Aminu Wali ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar PDP na kasa da su kakabawa tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike takunkumi kan ayyukansa da ka iya haifar da ruguza jam’iyyar.

Wali ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar a wani taron manema labarai a Kano.

A cewarsa, matakin na Wike ya riga ya yi wa jam’iyyar illa ta hanyar yin adawa da ita, wanda ya kai ga rasa yin galaba a zaben shugaban kasa na 2023.

Ya ce dole ne shugabannin jam’iyyar su yi aikinsu ta hanyar yin abin da ya dace wajen mu’amala da Wike tun kafin lokaci ya kure saboda ba shi da wata kima a jam’iyyar.

“Ya kamata shugabannin PDP su kira Wike ya ba da umarni ta hanyar dakatar da shi ko kuma a kore shi daga jam’iyyar.

Mafi muni da zai iya yi, ya riga ya yi. Mun sha kaye a zaben shugaban kasa na 2023 saboda ayyukansu.

Gwamnonin G5 sun hada kai suka yanke shawarar yin yaki da jam’iyyar. Menene darajarsu? A kasar Hausa ana cewa gara a baiwa mutum naira daya lokacin bukata da a ba shi naira goma idan ba ya bukata, domin a lokacin da ya ke bukata, naira daya ta fi masa daraja. ”

“Kwanakin baya, wani jigo kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya yi bayani dangane da rikicin jihar Ribas. Sai dai kash, daya daga cikin shugabannin jam’iyyar mu, Sakataren Yada Labarai na kasa, ya fito ya kalubalanci kalaman Alhaji Sule Lamido.

Wannan ya ba mutane irina mamaki matuka domin abin da Alhaji Sule ya fada shi ne gaskiya babu wani daga cikin mutanen da ke cikin rukunan shugabanci a jam’iyyarmu da ya ce. Mun fadi haka: fahimtar jam’iyyarmu ba ta da kyau kamar da.

“Alhaji Sule Lamido, ya fadi gaskiya kan rikicin Ribas da yadda jam’iyyar ta kasa shawo kan lamarin. Ribas dai jiha ce karkashin PDP; gwamnatin PDP ce. Wanne irin aiki shugaban kasa ke da shi wajen tunkarar matsalar jam’iyyar cikin gida? Gwamna Fubara dan PDP ne. Shi ne gwamnan jihar Ribas kuma yana samun matsala da ‘yan majalisar jihar. Wannan al’amari ne na cikin gida.

Me zai sa shugaban kasa ya sanya kansa cikin wani lamari na cikin gida?

“Ya kamata kungiyar gwamnonin PDP su marawa Gwamna Fubara baya don ya iya tsayawa da kafafunsa da kuma adawa da Wike. Na yi imani Gwamna Fubara, Allah ne ya ba shi mulki. A yau shi ne gwamna, don haka ya dauki matakin da ya dace.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here