Ma’aikatar harkokin kasar wajen Koriya ta kudu tace ‘yan Kasarta su 2 da aka yi garkuwa da su a Jihar Rivers ta Najeriya, sun shaki iskar ‘Yanci.
A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a ranar asabar tace tun a ranar 12 ga watan Disamba aka sace ‘yan kasar wajen, wadanda ma’aikata ne a kamfanin Daewoo Engineering & Construction Co…
Karanta wannan: Sojin Isra’ila sun bayyana cewa suna gwabza kazamin fada a kudancin Gaza
Hukumomin Koriya ta Kudu sun tabbatar da sakin mutum biyun inda suka kara da cewa suna cikin koshin lafiya.













































