Rundunar sojin Isra’ila tace dakarunta na ruwa da na sama sun kai hari kan wasu wurare a yankin Zirin Gaza inda suke gwabza kazamin fada.
Tace sojojinta a birnin Gaza sun kashe gomman ƴan ta’adda a musayar wuta daban-daban cikin sa’o’i 24 da suka wuce.
Sojojin sun kuma lalata wasu gine-gine guda biyu wadanda Hamas ke amfani da su a birnin Beit Lahiya da ke arewacin Gaza.
Karanta wannan: BCPG ta bukaci Tinubu da ya dakatar da shirin kara farashin siminti a 2024
Wannan na zuwa ne yayin da Falasdinawa ke cewa tankokin yakin Isra’ila na ci gaba da lugudan wuta a Gaza har cikin dare.
Ma’aikatar lafiya karkashin ikon Hamas a Gaza ta ce an kashe mutum 187 a wasu hare-hare cikin sa’o’i 24 da suka wuce.