ACF ta yi Alkah-wadai da harin jirgin sama da aka kai a Sokoto

images 2 7

 

Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta yi Allah-wadai da harin jirgin sama da aka kai a ranar Kirsimeti a garuruwan Silame da ke Jihar Sokoto, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 tare da jikkata wasu da dama.

ACF ta bukaci sojoji su sake duba dabarunsu wajen yaki da matsalar tsaro a yankin Arewa da kasa baki daya.

A cikin wata sanarwa da Sakatare na Yada Labarai na ACF, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya fitar, kungiyar ta bayyana damuwa kan musun da sojoji suka yi na kashe fararen hula, tare da neman a biya diyya ga wadanda abin ya shafa bisa ka’idojin shari’ar Musulunci.

Kungiyar ta yabawa gwamnatin Jihar Sokoto bisa daukar mataki cikin gaggawa, tare da kira ga gwamna Ahmed Aliyu da ya tabbatar da cika alkawuran da ya dauka ba tare da bata lokaci ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here