Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya gana da mambobin ƙungiyar gwamnonin APC a fadar sa da ke Abuja yau Laraba.
kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaitu cewa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa sanata Abdullahi Adamu, yana ɗaya daga cikin waɗanda suka halarci taron, wanda aka yi shi tsawon sa’a guda.
Amma ba a shaida wa sakamakon taron wanda ya sami hallartar gwamnonin da aka zaba a karkashin tutar jam’iyyar APC, sai dai har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoton ba a shaida wa manema labarai abinda aka tattauna a taron ba.
Kamfanin NAN ya ruwaito cewa mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, wanda ake sa ran tantance shi a matsayin wanda za’a fafa ta da shi a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar a yau, ba a ga fuskar sa ba a gurin taron da aka yi a fadar shugaban kasa.
Gwamanan jihar Kebbi Atiku Bagudu, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC ya ƙi cewa komai akan sakamakon taron.
Haka kuma, kamafanin dillan cin labaran ya ruwaito cewa, an yi taron ne akan muhimman matsalolin da ke da alaƙa da babban taron da jam’iyyar zata gudanar a ranar 6 da kuma 8 ga watan Yunin mai kamawa.
Haka kuma NAN ya ce, shugaban ƙasa ya yi amfani da damar taron, ya tattauna nda su a kan zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa da jam’iyar zata gudanar a nan gaba don ganin an samu haɗin kan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar dama gwamnonin APC baki ɗaya.













































