Gwamnatin jihar Ribas ta janye amincewar da ta baiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na amfani da filin wasa na Adoki Amasiaemeka dake Igwurita Ali a karamar hukumar Ikwerre wajen yakin neman zaben shugaban kasa.
Kwamitin yakin neman zaben ya tsara ranar 11 ga Fabrairu, 2023, don yakin neman zaben Atiku a fatakwal.
Gwamna Nyesom Wike makwanni biyu da suka gabata ya ba da izinin amfani da filin wasan domin yakin neman zabe amma da sharadi.
Sai dai a wata wasika mai dauke da kwanan watan 31 ga watan Junairu, 2023, da kuma aikewa darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben Atiku kuma gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Tambuwal, kwamishinan wasanni na jihar Ribas, Barista Christopher Green, ya ce bayanan sirri sun nuna cewa kwamitin yakin neman zaben Atiku na hada kai da Dan takarar gwamnan APC , Arch. Tonye Cole, don raba kayan aikin da aka amince don yakin neman zaben shugaban kasa.
Kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar a jihar Ribas, Dokta Lenu Nwibubasa, don jin ko ya samu wasikar ya ci tura domin bai amsa kira ko amsa sakon da aka aike masa ba.













































