Kotun Koli Ta Soke zaben fidda Gwanin Dan takarar Gwamnan APC

Senator Emmanuel Bwacha
Senator Emmanuel Bwacha

Rahotanni sun ce kotun koli ta soke zaben Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Taraba.

Kwamitin alkalan mai mutum biyar karkashin jagorancin Kudirat Kekere-Ekun ta yanke hukuncin.

Wata babbar kotun tarayya da ke Jalingo a jihar Taraba ta fara korar Bwacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a watan Satumban 2022 a karar da David Sabo Kente, dan takarar gwamna ya shigar.

Kotun koli ta tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke na cewa jam’iyyar APC ba ta gudanar da wani sahihin zaben fidda gwani na gwamna a jihar Taraba da ya samar da Bwacha a matsayin dan takarar gwamna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here