Babbar kuton Kano ta sa ranar 28 ga watan July domin yanke wukunci kan zargin kisan Hanifa mai shekaru biyar a duniya, wanda ake zargin shugaban makarantar Noble Kids Academy, Abdulmalik Tanko, da aikatawa.
Gwamnatin jihar Kano na tuhumar Tanko, Hashim Isyaku mai shekaru 37 da kuma Fatima Musa mai shekaru 26 bisa hadin kai wajan aikata ta-addan ci, garkuwa, tare da kuma buye gwarar Hanifa bayan an kashe ta.
Sai dai kuma wadan da ake zargi basu amsa lefin su ba
Tun da fari dai ana zargin shugaban makarantar Nobel Kids Comprehensive College, Abdulmalik Tanko da yin garkuwa da Hanifa tare da kashe ta, bayan ya boyeta a gidan sa da ke Tudun Murtala a karamar hukumar Nassarawan Jihar Kano.













































