PDP: Atiku ya fara ganawa da ‘yan takarar da ya kayar a zaben fitar da gwani.

Atiku with other PDP presidential contestants
Atiku with other PDP presidential contestants

Dan takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya fara ganawa da ‘yan takarar da yakayar a zaben fitar da gwani da jam’iiyar PDP ta gabatar ranar Lahadi a garin Abuja.

Kamfanin dillan cin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa Abubakar ya ziyarce gwamnan Jihar Rivers Nysom Wike a gidan sa dake Abuja ranar litinin.

Tun da fari, dan takarar ya ziyar ce gwamna Aminu Tambuwal wanda shine ya janye masa ya yin da ake tsaka da gudanar da zabe.

Atiku Abubakar ya wallafa a shafin sa naTweeter cewa,  ziyarar da yake yi cigaba ne na kokarin sa don ganin cewa ya tafi kowa na jam’iyyar.

Atiku Abubakar ya sami kuri’u 371 wanda ya bashi damar zuwa na daya, yayin da Wake yazo na biyu da Kuri’u 237, inda kuma tsohon shugagaban majalisar dattijai ta kasa, Abubakar Saraki yazo na uku da kuri’u 70.

A yayin da yake jawabi a ranar Asabar, Atiku Abubakar ya  yi alkwarin cewa zai yi aiki da ‘yan takarar da ya kayar kafada da kafada.

”Bara nayi amfani da wannan dama nayi kira ga abokanan da suka kara dani a zaben fitar da gwani, na tabbatar musu da cewa a shirye nake da nayi aiki dasu kafada da kafada a wannan jam’iyyar  tamu da kuma gwamnatin da zamu kafa a nan gaba.”

”Haka kuma, ‘yan uwana ‘yan kasa ina yaba muku bisa kokarin ku na kare martabar dimukuradiya a wannan jam’iyyar.’’

”Zan bi duk wasu hanyoyi don ganin nai aiki daku kafada da kafada, domin mu kai jam’iyyar mu  zuwa  ga cin zabe.’’

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here