Yadda wata kwararriyar Akanta mai shekaru 47 ta hallaka kanta

images 8
images 8

Alamu sun bayyana, cewa matar da aka ruwaito ta kashe kanta, mai suna Afolake Abiola, yar shekaru 47 a ranar Juma’ar da ta gabata, a gidanta da ke lamba 1, Abayomi Kukomi Close, Osapa London, a yankin Lekki na jihar Lagos, tana dauke da wani yanayin rashin lafiya, baya ga bacin rai.

Wasu mazauna yankin sun tabbatar da hakan lokacin da jaridar Vanguard ta ziyarci, wajen.

Sai dai ’yan uwanta na kusa sun ki yin magana lokacin da aka tuntube su, inda suka bayyana cewa suna kokarin samun waraka daga mummunar illar da rasuwarta ta haifar musu.

Marigayiya Abiola, wanda ke zaune a wani gida mai dakuna uku a ciki, ta kasance kwararriyar Akanta kuma ta yi aiki da daya daga cikin kamfanonin sadarwa, na GLO, sama da shekaru 15.

Daya daga cikin masu haya a jerin gidajen da take, ma’aikacin gwamnati mai ritaya, Mista Patrick Olumhense, wanda ya yi magana da Vanguard, ya ce: “Mu makwabtanta ne kawai, ba dangi ba. Ba mu san labarin rasuwar ba sai da ‘yan uwanta suka tashe mu a safiyar Labari ne mai ban tausayi”.

Ta kasance makwabciyar mu kuma mai kyautatawa a gare mu duka.

Amma tana son zama ita kadai. “Ba ta da abokai da yawa, ban da kanwarta, wadda ta kan zo ta zauna da ita a nan.

“A baya dai ta kasance tare da kaninta wanda ya gina gidansa, ya yi aure kuma ya kaura da matarsa”.

“Amma a cikin shekaru biyar da suka wuce, ta kasance ita kadai. “A gaskiya, ta bayyana kamar wanda ke da kalubalen tunani. Kafin mahaifinta ya rasu, mukan gan shi da sauri ya gangaro gidan a wasu lokuta da ake ganin an kai mata hari. Ya kwantar mata da hankali, ya dauko mata wani irin magani ta sha sannan sai ta dawo ta fara rayuwa ta yau da kullum.

“Hakan ya faru na dan lokaci, har sai da mahaifin nata ya mutu”.

“Tun da mahaifinta ya rasu, babu wanda yake mata irin wannan hidimar, sai kanwarta da ta zo sau daya. “A gare mu a matsayinmu na makwabta, mun san da wannan matsalar”.

A duk lokacin da yanayin ya zo, mukan tuntubi ‘yar uwarta ko kaninta. Amma a wannan karon, ba ta nuna alamun cutar ba, ”in ji Makwabcin ta.

Jami’in Tsaron dake Yankin da gidan yake

Lokacin da Junior mai shekara 25 ya yi nasarar yin magana, ya ce, “Mutuwar Madam ta ba ni mamaki. Ita ce irin macen da ba ta son hayaniya.

“A gaskiya ina shirin barin wannan aikin ne domin ita kadai ce take taimaka mani a gidan nan”. Inji Junior

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here